INA SO NA FARA KOYON TECH SKILLS, DA WANE ZAN FARA ?: Amsa ga masu wannan tambayar
Mutane da yawa da suke mani wannan tambayar, cewa suna son su fara koyon Tech skills, amma sun rasa ta ina zasu fara, ga amsar tambayar ku nan, awannan post din.
Duk lokacin da kake so ka koyi wani ilimi, kana bukatar ka koyi foundation nashi, wanda sune basics na ilimin, ta yadda idan kasamu wannan foundation din mai kyau, kusan kome zai zo maka da sauki, kuma shi zai haska maka, ka san inda zaka tafi.
Alhamdulillahi, na yi videos da yawa, tun daga Basics na Computer har zuwa advance level, inda mutun insha Allah zai samu aiki, ko zai iya neman kudi da abun da ya koya, kuma zai iya ci gaba da tafiyar sa dakansa, muddin ya koyi wadannan skills din da kyau.
Zanyi guiding naku na yadda Youtube videos bawa suke, ga duk wanda yake so ya fara Tech journey nasa.
Da farko dai idan ka shiga Youtube channel tawa mai suna Ahmad Aminu Ahmad, kaje karkashin Playlist, to ka nemi folder mai suna BEGINNER LEVEL, aciki akwai videos guda hudu, ka kalle su duka, saboda nayi bayani kan Basics na Computer har da yadda ake formating da installing na New windows.
Idna ka gama da wannan playlist din na Beginner Level, ka nemi playlist kuma mai suna BASICS COMPUTER SKILLS TRAINING, a wannan playlist din akwai videos guda 11 a ciki, shima tun daga what is computer wannan training din ya fara har zuwa karshe.
Idan ka gama kallon duka wadannan playlists din guda biyu, idan kana son ka koyi IT Employability skills Bootcamp kai tsaye, to kanemi playlist na IT EMPLOYABILITY SKILLS BOOTCAMP FOR WOMEN 1.0 akwai videos 27 a ciki, da kuma GRADUATES IT EMPLOYABILITY SKILLS BOOTCAMP 2024 shi kuma akwai videos 13 aciki, ka kallesugaba daya.
Idan ka gama wadannan Basics din duka, kuma kana so ka ci gaba, musamman a harkar Data Analytics, to ka nemi series nawa na KOYI EXCEL akwai videos 65 a ciki.
Idan kagama shi duka, ka nemi playlist na DATA ANALYTICS BOOTCAMP 2024 akwai videos 63 a ciki, ka kallesu, so, insha Allah zaka samu enough skills a fannin Data Analytics.
Idan kuma ba Data Analytics kake so ba, idan ka gama Basics na sama, sai ka fara da playlist na KOYI HTML videos 51, idan ka gama kaje KOYI CSS videos 51 shima, sai kaje KOYI JAVASCRIPT videos 31.
Kana kuma iya fara da videos na koyon Webiste using Content Management System (CMS), ka duba playlist na WEB DEVELOPMENT.
Akwai sauran beginner level musamman ga masu karatun Computer, kamar su KOYI SQL videos 43, KOYI PYTHON videos 42, playlist na SPSS, da sauran su.
Da fatar wannan zai taimakawa masu neman ta ina zasu fara koyon Tech Skills.
You can share with others or tag your friends.
Allah kasa mudace.
Stay blessed.
Ahmad Aminu Ahmad esq.
+2347066309565
[email protected]