WANDA YA SAN KANSA YA FI WANDA YA SAN DUNIYA !!!
Sanin kanka ba wai ka san sunanka, asalinka ko matsayinka a cikin mutane kawai ba ne. Sanin kanka shi ne ka fahimci wanene kai, me kake iya yi, inda raunin ka yake, da kuma irin mutumin da kake son zama.
Mutum ya fahimci halinsa, rauninsa, ƙarfinsa, iyawarsa da gazawarsa, maimakon ya shagaltu da sanin komai game da mutane da abubuwan duniya amma bai san kansa ba.
Akwai bambanci tsakanin sanin duniya da kuma sanin kai.
Mutum na iya sanin abubuwa da yawa game da duniya; ya san halayen mutane, ya san dabarun rayuwa, ya san yadda ake samun kuɗi da yadda ake mu’amala da mutane. Amma idan bai san kansa ba, duk wannan ilimin ba zai wadatar da shi ba.
● Wanda ya san kansa ya san abin da zai iya da abin da ba zai iya ba.
● Ya san kurakuransa, don haka yana ƙoƙarin gyara kansa.
● Ya san ƙimarsa da iyakokinsa, don haka ba ya raina kansa ko ya ɗaukaka kansa fiye da kima.
● Ya san cewa rayuwarsa tana da iyaka, don haka ba ya barin son duniya ya shagaltar da shi daga abin da zai amfane shi.
● Ya fi mayar da hankali wajen gyaran zuciyarsa da halayensa fiye da bibiyar kura-kuran wasu.
Sanin kai shi ne ka san ƙimarka ba tare da girman kai ba, raunin ka ba tare da raina kanka ba, kuskurenka ba tare da kare shi ba, da kuma manufarka ba tare da kwaikwayon kowa ba.
Wanda ya san kansa ba ya rayuwa domin ya burge mutane. Ba ya auna darajarsa da yabo ko suka. Ya san cewa wasu za su fahimce shi, wasu kuma ba za su fahimce shi ba, kuma hakan ba zai sa ya rasa kansa ba.
Ka san lokacin da ya kamata ka yi magana, da lokacin da shiru ya fi maka alheri. Ka san abin da ya dace da kai, da abin da ya kamata ka nisanta. Ka san cewa ba duk wata dama ce ni’ima ba, kuma ba duk abin da ka rasa ba ne asara.
Duniya tana koya maka yadda za ka san wasu; hikima kuma tana koya maka yadda za ka san kanka.
Saboda haka, kafin ka yi ƙoƙarin fahimtar duniya, ka fara fahimtar kanka. Domin wanda ya san kansa, ya san inda yake, ya san abin da yake nema, kuma ya san abin da bai kamata ya bari ya ɓata masa hanya ba.
Sanin duniya ilimi ne; amma sanin kai hikima ce.
✍️ Faridah Bintu Salis
(Bintus-sunnah)