DUK MAI SON KARE KUNGIYAR IZALAH RESHEN KADUNA AKAN INTERFAITH!
1-Idan wani yazo da dabaru na kare kungiyar izalah akan interfaith ga wasu Abubuwa da zaka ritsa shi akai.
2-Tambayoyi kamar haka:
Na farko:Shin Interfaith din da ya shahara a wajen cibiyoyin da sukeyi a duniya zamu dauki isdilahin su don fito da ma'anar ta ,ko izalah zamu jira ta fada mana Nata interfaith din sai mu kyale Abunda ya zamanto Urfin masu yi?
3-Meye Banbancin Dake tsakanin Zaman da shuwagabannin sukeyi da bangarorin da suke jagoranci da zaman da cibiyoyin interfaith sukeyi a Duniya?
4-Shin a cibiyoyin interfaith Ana iya sukan kafuri akan wani Abu da yake Kai ba daidai ba ?
Kamar yadda A zahirin ma'anar Tattaunawa tsakanin Musulunci da kafurai yake nuna Tattaunawa ne na Da'awah,zaka nunawa kafuri batan shi ,irin yadda masu Dibate sukeyi .
5-Shin Ana iya samun wani kafuri ya musulunta A sanadiyyar Cibiyoyin interfaith musamman pastoci kamar yadda Ake samun su musulunta idan ana Muhawarah ta Da'awah dasu?
6-Ya fada maka Abubuwa biyar na manufofin cibiyoyin interfaith na ko wace kasa ko ko wane cibiya da ya sani a duniya ?
15/08/2026
Siddeeq Ahmad Abubakar Kumo
Sadiq Ahmad Abubakar Kumo
@highlight