Menene NFT (Non Fungible Token)...
Yau dai bari mu leka cikin NFT wato "Non Fungible Token". A cikin Crypto da Blockchain industry idan aka ce NFT ana nufin token din da baya rabuwa, token din da ba'a iya fasa shi, ko a iya raba shi gida biyu, a faskara shi ko a 'bangara shi. Yadda yake guda daya to haka zai cigaba da zama a matsayin abu daya babu wani irin sa.
NFTs crypto tokens ne da ake iya ajiye video clip a cikin su, ko hoto, ko zane ko wata murya ko kuma wani Art work, kuma a dora shi akan blockchain domin a adana shi. NFTs ba'a iya exchanging dinsu da wani Crypto ya zama madadin su kai tsaye, sai dai ana iya biyan kudi a bayar dasu, kamar ka bayar da TON a baka NFT.
Domin mu fahimci NFT sosai, zan bayar da misali da Fungible Tokens, idan aka ce Fungible Tokens sune irin su Bitcoin, Ethereum, BNB, CORE, Solana da sauran su, misali:
~ A yanzu Solana kwaya daya (full unit) yana kan farashin Dala 157, idan bani da kudin da zan sayi SOL guda daya zan iya sayan wani bangare nasa kamar 0.5 SOL, 0.02 SOL, haka ma Bitcoin zan iya sayan 0.05 misali, to su NFT ba zaka iya sayan su irin haka ba.
Ba zaka iya yankan 0.3 na wani NFT ka saya ba, sai dai ka saya guda (full unit) to shine Non Fungible din, ba'a iya tsaga shi ko fasa shi a sayi wani bangare kamar yadda ake iya sayan 0.1 BNB ko Bitcoin.
NFTs suna dauke da digital value na wani abinda yake akwai shi a zahiri, misali "Durov Cap" akwai ta a zahiri amma anyi mata kudi anyi tokenizing dinta Online. Idan ka sayi na Online din kamar exactly ka sayi wancan na zahirin ne. Kuma yana iya kasancewa zallan digital value ne dashi ba lallai ya zama akwai shi a zahiri ba.
Kamar Digital Land wanda kamfanin SandBox suka yi NFT dinsu a 2022 kuma suka yi daraja sosai. Duk wani NFT daka gani to shi kadai ne babu irin sa sai dai mai kama dashi amma ba exactly shi ba, misali:
~ Bitcoin akwai irin sa exactly har guda miliyan 21,000,000 babu abinda ya bambanta wani Bitcoin da wani, amma NFT kwaya to kwaya dayan ne kawai, misali: za'a iya yin NFT na Sarkin Kano akan TON blockchain, Sarki Ado Bayero, sannan za'a iya yin NFT na Sarki Aminu ko Sarki Sanusi, kaga waɗannan mutane ne daban daban.
NFT na farko da aka fara yi Crypto da Blockchain industry shine wanda aka yi proposing akan Ethereum a 2018, proposal din ya fito da EIP-721 daga baya DAO suka amince ya koma ERC-721 kamar dai yadda kowa yasan yadda ake yin proposal akan Ethereum, daga EIP zuwa ERC.
Kamar yadda ake da kasuwanni Crypto CEX da DEX to suma haka NFT suke da kasuwannin su. Wanda aka fi sani a duniya itace OpenSea, tana kan blockchain fiye da 20, kamar Bitcoin, Ethereum, BNB, da sauran su.
Akwai irin su Getgems akan TON, har wa yau akwai kasuwar Fragment akan TON, akwai Magic Eden da Tensor da Nifty duk akan Solana, akwai XRP Cafe akan XRP chain.
~ Akwai Rarible da Foundation akan Ethereum. Suna nan da yawa gaskiya.
Sannan NFT suna da "Rarity" wato yanayin yadda suke a kasuwa, zai iya zama suna da yawa kamar daga 1 zuwa 100 suna bangaren high Rarity, wato basu da yawa. Gwargwadon ƙarancin NFT a kasuwa gwargwadon darajar sa, idan suna da yawa zaka ga Rarity dinsa is Common, to ba lallai yayi daraja sosai ba.
Idan kuma wani abu ne daban kamar Expensive, Light, ko Legen ko Gifted zai iya yin daraja gwargwadon irin darajar abinda ke kunshe cikin NFT din da kuma darajar da aka bashi tun da farko.
A yanzu haka TON ya zarce kowane blockchain wajen daily trade na NFT a duniya, idan akwai wanda ya zarce shi bai wuce Ethereum ba, tun bayan NFT na Gift da Pavel Durov ya raba. Kuma wani abun burgewa shine Telegram Collectibles Gifts ana iya Swapping dinsu Off-Chain.
NFT gifts da TON suka yi suna kan wallet guda dubu 184,021 kuma rabin su anyi trade dinsu. Telegram Stars da TON coin da kuma Gift suna daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen motsawar TON blockchain. Sai dai muna ganin Stars din zasu iya kawo tsaikowa TON coin, duk da cewa bamu san tsarin da suka yi ba nan gaba.
Ya ake yi NFT yayi daraja?
Dayan uku ne: