Yau akan BSC, CZ ya ƙona wannan token ɗin mai suna Marscoin guda… — GALMA CRYPTO NETWORK — TG.ME

Yau akan BSC, CZ ya ƙona wannan token ɗin mai suna Marscoin guda 4,444 daga wallet ɗin sa da yake riƙe da 70% na token ɗin da aka tura masa.

Nan take token ɗin ya tashi zuwa 18 million MC a ƴan mintuna, saboda mutane da yawa da suke tracking wallet ɗin.

Yanzu haka dai token ɗin ya faɗo zuwa $10 million. Wasu suna zargin meyasa bai ƙona duka 70% supply ɗin ba ya ƙona 4444, mutane na ganin hakan alama ce ta wani abu.

A gefe guda kuma wasu suna ganin dama kwanaki kaɗan da suka wuce yace zai siya wasu memes ko ya siyar, har yayi addu'ar 'may the best memes win'. Shin ko dai abinda ya faɗa ne yayi akan Mars?

Me kuke tunani? Me kuke gani? Shin Marscoin daga nan sauka zaiyi ko kuma zaici gaba da tashi sama?

Ku faɗa mana ra'ayin ku.
❤8
August 16, 2026 595