PI NETWORK YA SHIGA GOGAYYA DA SU APPLE, GOOGLE DA MICROSOFT!!!
Abubuwa uku mahimmai da pi network ta gabatar a jiya ranar bikin Pi2day🔥
Yayin da mafi yawancin mutane a cikin harkar Crypto suke zuba ido suna jiran ganin farashin Pi yayi tashin gwauron zabi, su kuwa Pi Core Team babban shiri suka fito da shi na yadda Pi zai zama babban jigo a daukacin duniyar Intanet (Web2 da Web3).
A bukin Pi2Day na jiya, Core Team sun saki wasu manyan abubuwa guda uku masu girgiza duniyar crypto da internet, wadanda ke nuna cewa Pi ba wai coin na gama-gari ba ne kawai, asali ma yana so ya kafa daular da zata raba gari da su Apple, Google, da Microsoft
Ga muhimman abubuwa guda uku da ya kamata kowane Pioneer ya sani:
👇
(1) SOLO HOST (Juya Kwamfutarka ta Zama Supercomputer) 💻
Wannan wani sabon tsari ne a Pi Desktop (na kwamfuta) wanda zai baiwa masu ƙera manhajoji (Developers) damar kawo apps na AI (Artificial Intelligence) da manhajar raba karfin kwamfuta (Distributed Computing).
Kamar yadda mutane ke amfani da kwamfutar su wajen gudanar da Node na Pi, yanzu zasu iya amfani da ita wajen gudanar da manhajar AI (misali kamar wani app da ake ƙira Hermes). Sirrinka da bayananka suna nan a kwamfutarka ba tare da sun tafi uwar garken (server) wani kamfani ba.
Wannan kalubale ne ga Manyan Kamfanoni, saboda irin su Google da Microsoft suna kashe biliyoyin daloli wajen gina "Cloud Servers" na AI. Amma Pi yana so ya hada ƙarfin kwamfutoci sama da 420,000 na Pioneers don su zama babbar kwamfuta guda ɗaya ta duniya ba tare da mallakar wani babban server ba.
(2) PI SIGN-IN (Mabudin Intanet Kamar "Sign in with Google") 🔑🌐
Wannan tsari ne da zai ba ka damar amfani da asusunka na Pi (Pi Account) wajen yin rajista ko shiga (Login) a sauran jafar yanar gizo (websites) da apps na waje da ba na Pi ba, ba sai ka tsaya kana ƙirƙirar sabon password ko username a kowane website ba. Da zarar ka danna "Sign in with Pi," ka shiga ke nan cikin sauƙi ta hanyar amfani da Pi Browser dinka.
Kamar yadda kake gani ana sa "Sign in with Google" ko "Apple" a kafar yanar gizo, yanzu Pi ya shigo wannan sa'ar. Bambancin shi ne, Pi yana zuwa ne da asusun da aka tabbatar na mutum ne da aka tantance (bashi da bot ko fake accounts), kuma yana da alaƙa da Pi Wallet don biyan kuɗi na gaba, ba kamar yadda a Google zaka buɗe account barkatai kai kaɗai ba.
(3) PI VERIFY (Zama Kamfanin Tantance Mutane Na Duniya)
Pi Network ya buɗe tsarin sa na KYC (tantance bil'adama) ga sauran kamfanonin waje da bankuna na intanet (Fintechs) wadanda suke bukatar tantance mambobinsu.
Kamfanonin waje zasu rika amfani da fasahar Pi wajen gano mutanen gaskiya domin magance zamba da fake accounts. Kuma babban abin farin cikin shi ne, Wadannan kamfanoni na waje zasu rika biyan kudi ne da Pi Coin domin amfani da wannan service ɗin na PiVerify.
Pi ya riga ya tantance mutane sama da miliyan 18 a kasashe sama da 200. Yanzu Pi ya daina zama mai neman KYC, ya koma shi ne mai bayar da KYC (KYC Provider) ga duniya. Wannan zai kawo babban sauyi Na use case (utility) da bukatar Pi Coin a kasuwa ta zahiri.
Yayin da muke ke jiran yaushe za a bude Mainnet ko nawa ne farashi?, mu sani cewa darajar crypto tana ginuwa ne akan amfaninta (Utility). Pi Core Team suna aiki ta ƙuru wajen faɗaɗa utility da use case, suna gina ababen more rayuwa ne na intanet wanda zai tilasta wa manyan kamfanoni amfani da shi.
Idan Pi ya zama shi ne mabudin shiga websites, shi ne mai bada karfin AI, kuma shi ne mai tantance mutane a duniya... To batun farashi lokaci ne kawai in sha Allah. Babagana Aisami✍️
Allah Ya tabbatar mana da alherin Pi, Allah Ya sa muna daga cikin wadanda zasu amfana mu kuma amfani al'umma🙏