New Tax Law, rubutu na 'daya:
Idan dokar ta fara aiki:
1. Ba za'a bude Account a Banki ma kowa ba sai mutum yana da Lambar shaidar biyan Haraji idan yana cikin masu biyan.
2. Kamfanonin kasashen waje dake Nigeriya dole su dinga biyan Haraji har akan ribar da suke samu.
3. Idan dokar ta fara aiki, za'a umarci Bankuna su dinga tura bayanan wadanda suke yin hada hadar kudi fiye da Naira miliyan 25 a duk wata uku, idan kamfani ne yayi hada hadar Naira miliyan 100 to shima za'a tura bayanan sa ma gwamnati.
4. Duk wanda yake samun kudin shiga (income) da bai kai Naira dubu 800,000 ba babu shi a cikin biyan harajin (Personal Income Tax).
5. Kamfanonin da suke samun 'kasa da Naira miliyan 50 a shekara babu su a cikin biyan harajin ribar da suke samu (Profit).
6. Za'a kafa kotunan da zasu dinga warware kararraki, korafi da matsalolin Haraji tsakanin mutane, tsakanin gwamnati da gwamnati, kamar jiha da karamar hukuma ko tsakanin kamfanonin da hukumar tattara Haraji.
7. An bada dama wa jihohi su dinga karban Harajin wadanda suke rayuwa a jihohin su.
8. Za a rika karban Harajin ne ta cikin Asusun Bankin mutane da zaran lokaci yayi zaka ga Debit alert.
9. Manyan kamfanonin dake hada hadar Naira biliyan 50 zasu rika biyan kaso 15.
10. Dukkanin sunayen kasuwancin "Business Names" dole su mallaki "e-invoicing" da kuma "VAT systems real time".
Mu hadu a rubutu na biyo domin cigaba.
Copied
October 5, 2025 171