Sabuwar dokar haraji da shugaba Tinubu ya sawa hannu, zata fara aiki a 2026. Ku gyara zama ku karanta rubutun nan a tsanake. This is a very very serious issue wlh.
Mataki na farko, idan abinda ka samu a shekara bai haura Naira dubu dari takwas ba (โฆ800,000) to babu haraji a kanka.
Mataki na biyu, idan abinda ka samu a shekara ya haura Naira dubu dari takwas amma bai wuce Naira miliyan uku ba (โฆ3,000,000) to dubu dari takwas (โฆ800,0000) babu haraji a kanta, amma abinda ya hau kai za'a dauki kaso sha biyar cikin dari (15%) nasa a matsayin haraji.
- Misali, in Naira miliyan daya da dubu dari uku ka samu a shekara, Naira dubu dari takwas ba za'a dau mata haraji ba amma sauran Naira dubu dari biyar (โฆ500,000) din da ta hau kai za'a dauki 15% dinta (wato Naira dubu saba'in da biyar โฆ75,000) a matsayin haraji. Wannan shine harajinka.

October 3, 2025 48