A bidiyon da nayi wanda na nuna cewa market cap na token ba shine… — SCTv Africa — TG.ME

A bidiyon da nayi wanda na nuna cewa market cap na token ba shine asalin kudaden da mutane suka saka akan token ba. Ga wani misali 👇

A dazu, $SUNUSI yana market cap $42k, sai wata wallet ta sayi $SUNUSI na $981 da kuma $1629, jimillah ya kama $2610 kenan. Shigar wannan kudi yasa market cap ta tashi daga $42k zuwa $65k. Kenan dai market cap ta karu da $23k.

Wancan bidiyon da nayi asalinsa yakai mintuna 19. Amma daga baya na yayyanke shi zuwa mintuna 5 kacal. Saboda masu korafin cewa bidiyona yana tsayi. Amma achikin asalin bidiyon nayi bayanin yanda mutane zasu gane asalin kudaden mutane dake kan tokens, musamman Meme tokens.

Domin sanin asalin kudaden dake kan token, kana bukatar ka fahimchi market cap, liquidity da kuma volume. Da kuma alaqar dake tsakaninsu.

Misali, token da yake da 100M supply, kuma yake akan farashin $0.1, zai kasance yana da market cap $10M. Idan ya kasance yana da karanchin liquidity da volume, sai wani ya sayi token din na $10k. Hakan zai iya sawa farashin token ya tashi zuwa $0.15. Kenan market cap ta koma $15M, market cap ta karu da 50%, wato $5M saboda $10k ta hau kan token. Kamar hakane kuma $10k zata sauka daga kan token din, hakan zaisa yayi mummunar faduwa lokachi guda.

Duk wayannan abubuwan ya kamata Dex trader ya dinga kiyayesu kafin ya shiga token.

A kula: Banida masaniya akan wannan wallet data sayi $SUNUSI na $2610.
❤36🔥4👍3👎3
August 25, 2026 2.8K 1 5