Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Barka da Juma’a, ’yan… — Majaalisu Daril Hadith wal Athar, Potiskum! — TG.ME

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Barka da Juma’a, ’yan uwa masu albarka. Ina yi muku fatan alheri da fatan Allah Ya ci gaba da shiryar da mu, Ya datar da mu a kan dukkan abin da Ya yarda da shi. Kamar yadda bayanin da ya gabata Alhamdulillah, na kammala wannan daura mai albarka cikin nasara. Ina kuma farin cikin yi wa ɗaliban ilimi da sauran masu kishin neman ilimi bushara cewa, in Allah Ya yarda, za a ci gaba da shirya irin wannan daura mai albarka a duk lokacin hutun makarantun Boko na yara, wato sau uku a cikin shekara. Haka nan, za a ci gaba da ɗaurorin yini guda da aka saba gudanarwa, tare da karatun kwana na wata-wata, domin ci gaba da ƙarfafa neman ilimi, tunatarwa da kuma ƙara kusanci da Allah Maɗaukakin Sarki. Muna roƙon Allah Ya sanya wannan daura ta zama sanadin ƙaruwa da ilimi, kyautata aiki da kuma samun albarka a rayuwarmu. Ya sa abin da muka koya ya amfanar da mu, ya amfanar da iyalanmu da al’ummarmu baki ɗaya. Allah Ya saka wa malamummu namu da mafificin alheri. Ya ƙara musu lafiya, tsawon rai da albarka a cikin rayuwarsu da iliminsu. Ya saka musu da alheri bisa irin wannan ƙoƙari da hidima da suke yi mana, suna raba mana ilimin da Allah Ya hore musu kyauta ba tare da gajiyawa ba. Allah Ya ba mu ikon fahimtar abin da suke koyar da mu, Ya ba mu ikon aiki da shi, Ya kuma sa mu zama masu isar da alheri ga waɗanda suke kewaye da mu. Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya amsa addu’o’inmu, Ya ƙara haɗa kanmu a kan alheri da neman ilimi.

August 28, 2026 99